Kano Assemblyy

Za a fara kasuwancin awanni 24 a Kantin Kwari

Gwamnatin jihar Kano tace ta gama shirin mayar da gudanar da kasuwanci a shararriyar kasuwar kantin kwari na tsawon awanni 24 a kullum.

Shugaban kasuwar ta kwari, Alhaji Hamisu Saโ€™adu Dogon Nama ne ya bayyana hakan bayan ya kare kasafin kudin hukumar gudanarwar kasuwar.

Dogon Nama yace daga cikin shirye -shiryen da suke yi domin tabbatar da kudirin na gwamnatin Kano, akwai wadata kasuwar da hasken wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da samar da ingantaccen tsaro yadda zasu dace da tanadin da gwamnati tayi.

Shugaban kasuwar yace zaโ€™a samar da wata manhaja wadda zata bawa โ€˜yan kasuwa damar cinikayya daga koโ€™ina a fadin duniya.

Kasuwar Kantin Kwari ta shara wajen sayar da sutura kama daga atamfofi, yadi, leshi da sauran nauโ€™in kaya, kuma ya shahara a nahiyar Afrika.