Gwamnatin jihar Kano tace ta gama shirin mayar da gudanar da kasuwanci a shararriyar kasuwar kantin kwari na tsawon awanni 24 a kullum.
Shugaban kasuwar ta kwari, Alhaji Hamisu Saโadu Dogon Nama ne ya bayyana hakan bayan ya kare kasafin kudin hukumar gudanarwar kasuwar.
Dogon Nama yace daga cikin shirye -shiryen da suke yi domin tabbatar da kudirin na gwamnatin Kano, akwai wadata kasuwar da hasken wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da samar da ingantaccen tsaro yadda zasu dace da tanadin da gwamnati tayi.
Shugaban kasuwar yace zaโa samar da wata manhaja wadda zata bawa โyan kasuwa damar cinikayya daga koโina a fadin duniya.
Kasuwar Kantin Kwari ta shara wajen sayar da sutura kama daga atamfofi, yadi, leshi da sauran nauโin kaya, kuma ya shahara a nahiyar Afrika.